Wasanni

Abubuwa shida da Najeriya ke bukata domin doke Iceland

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

A ranar Juma’a ne tawagar Super Eagles za ta fuskanci kasar Iceland a wasanta na biyu na gasar cin kofin duniya da ake bugawa a Rasha.

Najeriya ta sha kashi a wasanta na farko tsakaninta da Croatia da ci biyu da nema a wasan da suka buga a birnin Kaliningrad.

Nasara ce kawai za ta farfado da damar Najeriya domin ta kai zagaye na biyu a gasar.

Ga abubuwa shida da nake ganin za su taimakawa Najeriya a wasan da za a buga a birnin Volgograd da Iceland din:

1. Cin kwallo da wuri

A wasan kwallon kafa duk tawagar da ta soma zura kwallo, ta kan saka matsi ga abokiyar hammayarta abin da kuma zai kara wa tawagar kwarin gwiwa a cikin wasan.

Idan har Super Eagles ta soma cin kwallo ko kwallaye kafin Iceland, hakan zai zama mataki mai tasiri ga kasar.

Ganin cewa Najeriyar ba ta zura kwallo ko guda ba a wasanta na farko da Croatia, cin kwallo da wuri a ragar Iceland zai iya kashe gwiwar ‘yan wasan Iceland din.

Bugu da kari, idan har Musa da Iwobi da Iheanacho suka samu dama, to za su iya kasancewa wadanda za su fitar da Najeriya kunya.

2. Sauya salon wasa

A wasanta na farko, Najeriya ba ta nuna yunwar zura kwallo ba kamar yadda masu hasashe suka zata, wannan ya karya lagon wasu daga cikin ‘yan wasan da suka dan nuna azama.

Ina ganin cewa akwai bukatar a dinga yawaita kai hare-hare, sannan kuma ‘yan wasan su dinga sa himma da zarar kwallo ta shiga bangaren abokan hammaya saboda ta haka ne kawai za su iya zura kwallo.

Sannan su dinga amfani da ‘yan wasan gefe musamman Victor Moses, wanda ke da gudu sosai abin da zai iya karawa tawagar damar kai hare-hare babu kakkautawa.

3. Su guji jan kati

Duk karfin kasa a fagen kwallo, ta na iya fuskantar cikas da zarar an kori daya ko biyu daga cikin ‘yan wasanta. A don haka domin tabbatar da nasara dole sai ‘yan wasan Super Eagles sun yi taka tsan-tsan daga fuskantar fushin alkalin wasa.

Ko da yake ana bukatar su nuna kwanji amma dai dole ne sai sun bi a hankali musamman ‘yan wasan bayan Najeriya da na tsakiya.

Wannan kalubale ne ga Ogehnakoro Etebo da Abdullahi Shehu da William Ekong da kuma Leon Balogun, domin su ne ke tsare bayan. Idan har suka murza-leda cikin tsabta, hakan zai ba su damar kai wa ga gaci.

4. Maimaita tarihi

Sau daya tal Najeriya ta taba fuskantar Iceland a fagen kwallon kafa a duniya, kuma wasan bai yi wa Super Eagles dadi ba saboda Iceland ta samu nasara da ci uku da nema a wasan sada zumunci a shekarar 1981.

Sai dai kuma Najeriya na da tarihi mai kyau a kan kasashen Turai a gasar cin kofin duniya saboda nasarori biyar da Super Eagles ta samu a baya, duk a kan ‘yan kwallon Turai ne.

Misali nasara a kan Bulgariya a 1994, da Spain a 1998. Wannan matsayin da aka samu a shekarun baya, ya nuna cewa idan har tawagar yanzu ta mayar da hankali ita ma za ta iya shiga rukunin wadanda suka bai wa marada kunya.

5. Ahmed Musa da Mikel Obi

A wasan ta na farko a gasar ta bana, Ahmed Musa ya kasance ne a benci sai bayan an dawo hutun rabin lokaci aka saka shi. To watakila soma wa da Musa zai sa a dunga kai hari saboda yana da gudu kuma ba ya wasa idan ya tsinci kanshi a kusa da raga.

Sannan kyaftin din Najeriya, Mikel Obi bai taka rawar da aka za ci zai taka ba a wasansu da Croatia, watakila ya kamata a sauya masa matsayi daga dan wasan da ke taimakawa ‘yan wasan gaba zuwa wanda zai taimakawa ‘yan wasan baya kamar irin salon wasansa a Chelsea.

Hakan zai bai wa ‘yan wasa kamar su Ekong da Balogun su kare baya da kyau ba tare da an samu saukin kai wa ga golan Super Eagles ba.

6. Yanayi na zafi

A birnin Volgograd za a buga wasan, kuma garin na da dan karen zafi tamkar mutum ya na nahiyar Afirka ne.

Saboda haka kasancewar ‘yan Najeriya sun saba kwallo a cikin zafi da rani mai tsanani, dama ce a gare su fiye da ‘yan wasan Iceland wadanda ba su saba kwallo cikin wannan yanayin ba.

A don haka idan har tawagar Super Eagle ta yi amfani da wannan yanayin, ga alama za ta iya kai wa ga nasara.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi