Labarai Najeriya

An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Jam’iyyar APC

VOA Hausa
Daga VOA Hausa

An rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar APC na wa’adin shekaru hudu a karkashin shugabancin Adam Oshiomohle, tsohon gwamnan jihar Edo.

Sabon shugaban ya amince jam’iyyar nada kalubale amma yace, ya saba da warware takaddama.

Cikin shugabannin akwai wadanda aka sake zabensu irinsu sakataren jam’iyyar Mai Mala Buni.

Duk da rade-radin cewa baya marawa shugaba Buhari baya, an sake zaben Sanata Lawali Sha’aibu a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na arewa lamarin da yaba mutane mamaki.

Sanata Lawali ya ce idan mutum bashi da goyon bayan inda ya fito to ya manta da siyasa. Dangane da cewa Shugaba Buhari baya kaunarsa, yace masu hamayya ne suke rade-radin su.

Dan majalisar wakilai Ahmed Babba Kaita yace taron ya kayatar duk da caccakar da Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilai, ya yiwa Gwamnan Badaru na Jigawa, shugaban taron, cewa ya bar jama’a da kishirwa. Yace zaben shugabannin jam’iyyar ya tabbatarwa ‘yan Najeriya da duniya APC ta zo ke nan zata kuma zata ci gaba da kokarin ciyar da kasar gaba.

Matasa daga Kano da suka hada da Yahaya Gambo daga karamar hukumar Garko sun nuna damuwar rashin halartar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da hakan ba zai rasa nasaba ba da rashin jituwarsa da gwamna Ganduje. Yace a zamansa na dan jihar Kano yana son gwamnan Ganduje da Sanata Kwankwaso su zauna lafiya.

Shugaba Bubari ya godewa ‘yan jam’iyyar don kwazo. Shi ko uban jam’iyyar Bola Tinubu gugar zana ya yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar cewa sai canja sheka yake yi yayinda kuma tsohon shugaba Obasamjo ke neman canza shugabannin jam’iyya da karfin tsiya.

Game da mai rubutu

VOA Hausa

VOA Hausa

Aiko da Ra'ayi