Labarai Najeriya

Ana fama da rikicin kabilanci a Najeriya

DW Hausa
Daga DW Hausa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya za ta kafa sansanin ‘yan sandan kwantar da tarzoma a gundumar Gashish da ke karamar hukumar Barikin Ladi cikin jihar Filato.

Rikicin baya bayan nan da ya kunno kai tsakanin al’ummar Fulani da Berom shi ya janyo wannan mataki na kafa sabon sansanin na ‘yansandan kwantar da tarzoma a wani mataki na karfafa tsaro. Koda a watanin baya ma dai gwamnatin Najeriyar ta kafa wani sansanin sojojin sama a kauyen Kerang da ke Karamar hukumar Mangu, inda sojojin sansanin ke gudanar da tsaro ta sama a jihar Filato da ma wasu jihohi makwabta. Wasu al’ummar jihar ta Filato dai na ganin kafa sabon sansanin a Gashish, ba abin da zai canza yanzu kasancewar sansanin sojojin ma da gwamnatin ta kafa bai hana ci gaban tashe-tashen hankulan da ake fuskanta ba. Sai dai a cewar Hardo Yakubu Dabo Boro wanda shi ne hardon karamar hukumar Bakkos, yankin da ya yi iyaka da Barikin Ladin, kafa sabon sansanin ‘yan sandan zai taimaka har idan gwamnati da gaske ta ke.

Ziyarar shugaban kasa da mataimakinsa

Wannan dai shine karon farko da jihar Filato ta fuskanci mummunan yanayi na hare-haren ‘yan bindiga a gwamnatin Simon Lalong kasancewar a baya gwamnatin ta dauki matakai na zaman lafiya. Yanzu haka ma dai an kawo wa jihar Filato wani sabon kwamishinan ‘yan sanda, baya ga rundunonin sojoji da na ‘yan sanda da aka karo wa jihar. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ya ziyarci jihar Filato, inda shima shugaban kasa Mohammadu Buhari ya kai ziyara jihar Filato din, duk dai a kokarin daukan matakan magance wannan matsala na tashe tashen hankula a wasu yankunan jihar.

Kungiyar #BringBackOurGirls ta yi zanga-zanga

A yayin da mahukuntan Tarayyar Najeriya ke ci gaba a cikin daukar matakan kai karshen kisa na babu gaira babu dalilin, hakarkari yana kara dagawa a cikin kasar in da ‘yan fafutuka tabbatar da ‘yancin ‘yan mata na Chibok suka gudanar da wata zanga-zangar Allah wadarai da ci gaban kisan ba gaira a kasar. Duk dacewar dai an kira ta zanga-zanga ta mutun guda kuma jigon ta na zaman tsohuwar ministar ilimin Tarrayar Najeriya Oby Ezekwesili da ke neman tabbatar da kai karshen kisan na babu gaira babu dalili. An dai kai ruwa a cikin rana a tsakanin ‘ya’yan kungiyar ta BringBackOurGirls da suka nemi isa fadar shugaban kasar da nufin nuna bacin ransu da kuma jami’an tsaron da ke fadin ba hali. ‘Yan kungiyar dai sun ce ta yi baki ta kuma lalace game da yadda gwamnatin kasar ta zura ido ta kalli ta’azzarar kisan da ya kai shugaban kasar ziyara ta ba zata zuwa Filaton, amma kuma ya kasa kwantar da hankali na kungiyar.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi