Wasanni

‘Anya damben boksin yana da amfani?’

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Tsohon dan wasan kwallon kafa a Ingila kuma dan damben boksin a yanzu Curtis Woodhouse ya nuna tababarsa a kan amfanin damben bayan da Scott Westgarth ya mutu bayan damben da ya yi nasara.

Curtis Woodhouse ya ce mutuwar Scott Westgarth, ta sa shi yana tunani a kan cancantar wannan wasa na boksin, amma kuma ya ce ba zai taba shawartar wani ya daina damben ba.

Westgarth ya mutu ne a asibiti yana da shekara 31, bayan da ya kamu da rashin lafiya bayan damben da ya yi nasara a kan dan uwansa dan Ingila Dec Spelman a Doncaster ranar Asabar.

Woodhouse, mai shekara 37 wanda tsohon dan wasan kwallon kafa ne na tsakiya a kungiyar Sheffield United da Birmingham City wanda ya yi nasara a dambe 24 da ya yi daga cikin 31, ya ce boksin wasa ne mai ban mamaki matuka.

Tsohon zakaran damben na ajin manyan masu karamin nauyi na Birtaniya a da zai kara ne da John Wayne Hibbert a damben kambin matsakaita nauyi na Commonwealth a Doncaster, sai kuma aka fasa saboda mutuwar Westgarth.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi