Wasanni

Arsenal ta lashe Community Shield

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Kungiyar Arsenal ta yi nasarar lashe Community Shield, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea a bugun fenariti da ci 4-1.

Tun farko kungiyoyin sun tashi wasa kunnen doki 1-1, kuma Chelsea mai rike da kofin Premier ta fara cin kwallo ta hannun Victor Moses daga baya Arsenal mai kofin FA ta farke ta hannun Kolasinac.

Chelsea ta karasa gumurzun da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Pedro jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Mohamed Elneny.

Bayan da aka tashi daga fafatawar aka yi bugun fenariti, inda Arsenal ta ci kwallaye hudun da ta buga, ita kuwa Chelsea ‘yan wasanta Courtois da Morata suka barar da bugun da suka yi.

Kammala wasan na nufin za a fara gasar Premier ta bana a ranar 11 ga watan Agusta, inda Arsenal za ta karbi bakuncin Leicester City, ita kuwa Chelsea za ta kara da Burnley a ranar Asabar a Stamford Bridge.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi