Afurka Labarai

Aski ya zo gaban goshi a zaben kasar Kenya

DW Hausa
Daga DW Hausa

A ranar Talatar nan ake gudanar da zaben shugaban kasa a Kenya wanda shugaba Uhuru Kenyatta zai fafata da dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga dan shekaru 72 wanda ake ganin wannan ita ce takararsa ta karshe.

A wannan Talatar ce ‘yan kasar Kenya ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar a yayin da aka kawo karshen yakin neman zabe, Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya dukufa yin adu’o’i don neman nasara daga Ubangiji yana mai burin samun nasara a zaben. Ya ce : ”Mun zo don yin adu’o’i ga ubangiji don samun gudanar da zabe cikin lumana tare da neman zabin ubangji ta hanun ‘yan kasar Kenya.”

Hakan dai na zuwa ne a yayin da fiye da masu kada kuri’a dari biyu a yankin da ‘yan adawa suka fi karfi na Kisumu suka gudanar da zaman dirshin a ofishin hukumar zaben suna masu ikirarin babu sunayensu a rigistar masu zabe. Tuni a ka fara raba kayayyakin zabe daga shalkwatar zabe da ke Nairobi karkashin tsauraran matakan tsaro. An kuma jibge ‘yan sanda 150,000 don sa ido a zaben. Tsohon sakataran harkokin wajen Amirka John kerry da tsohuwar Firaministan kasar Senegal AminataToure sun gana da jami’an hukumar zaben kasar inda su ka bayyana gamsuwar su da shirye-shiryen zaben.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi