Wasanni

Barcelona ta fara La Liga da kafar dama

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Barcelona ta fara gasar La Liga ta 2017/18 da kafar dama, bayan da ta Real Betis 2-0 a wasan makon farko a ranar Lahadi a Camp Nou.

Barcelona ta ci Real Betis sau 13 suka yi canjaras biyu a wasa 15, kuma wasa bakwai a Camp Nou ta lashe su.

Kungiyar ba ta taba yin rashin nasara a wasan farko da ta buga a gida ba, ta ci wasa 27 ta yi kunnen doki biyu, kuma ta yi shekara tara a jere tana cin wasan farko a gasar La Liga tun daga kakar 2009/10.

Rabon da kungiyar ta ci wasan farko a ranar da aka bude gasar ta cin kofin Spaniya tun lokacin da Numancia ta doke ta da ci 1-0 a kakar 2008/19.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi