Labarai Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 400 a watanni biyar

DW Hausa
Daga DW Hausa

Kungiyar Amnesty International ta ce adadin fararen hula da suka mutu a Najeriya da Kamaru a sakamakon hare-haren Kungiyar Boko Haram daga watan Aprilu ya zuwa yau ya kai kusan mutane 400, adadin da ya nunka kusan sau biyu na wadanda suka mutu a cikin watannin biyar da suka gabaci watannin biyar na baya bayan nan.

Kungiyar ta Amnesty ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Talata inda ta ce lamarin ya yi kamari ne a sakamakon zafafa kai hare haren kunar bakin wake da Kungiyar ta Boko Haram ta yi a kasashen Kamaru da Najeriyar inda ta ce a watan Agusta kadai Kungiyar ta hallaka fararan hula fiye da 100 a Najeriya.

Sai dai Ta ce akwai yiwuwar adadin ya zarce haka kasancewa ba dukkanin hare haren da Boko Haram din ta kai ba ne aka bayyana a hakumance. Kungiyar ta Amnesty ta kuma ce daga watan Aprilu ya zuwa yau Kungiyra ta Boko Haram ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake har guda 30 a kasar Kamaru.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi