Afurka Labarai

Bola ta rufto ta kashe yara 17 a Mozambique

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

A kalla mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni a lokacin da bola ta rufto kansu.

Jami’ai a yankin sun ce wata bola da ta yi torokon mita 15 ita ce ta rufto, a lokacin da ake tafka ruwan sama da tsakar ranar Talata.

Wurin da bolar ta ke dai, matsugunin daruruwan matalauta da suka gina dakunansu da langa-langa ko katako ne.

Bolar ta bi ta kan wasu gidaje biyar da ke gefenta.

Ma’aikatan ceto na ci gaba da tona bolar ko za su sake samun wasu mutane ko kayan da lamarin ya rutsa da su.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa, Leonilde Pelembe, ya yi gargadin a yi taka tsantsan don ta yiwu akwai karin mutanen da bolar ta danne.

”Bayanan da muka samu daga hukumomin yankin sun ce mutanen da suke zaune a wurin bolar sun fi wadanda aka ba mu bayanin sun mutu, ” in ji Mista Pelembe.

Gundumar Hulene da ke Maputo, daya ne daga cikin wuraren da ba a damu da su ba a birnin. Yawancin mazauna gundumar su na samawa kansu matsuguni ne ko dai a can saman bolar ko kuma a gefe, ciki kuwa har da kananan yara.

Bolar ba wai ta na zame musu hanyar samun abinci ba ne kadai, har ta kan zama sanadin samun kudaden shiga kamar yadda wakilin BBC Jose Tembe ya bayyana.

Hadarin da ake jiran ya faru?

Sharhi daga wakilin BBC na Afirka a birnin Moputa Jose Tembe

Wakilin BBC ya ce tun ya na karami ya taso ya ga bolar a wurin, a shekarar 1980. Zai iya tuna lokacin da aka fara gine-gine a wurin.

Lokuta da dama, hukumomin yankin sun yi ta kokarin korar mutane tare da kwashe bolar. Duk lokacin da damuna ta kama, jami’ai na zuwa tare da bai wa mutanen wurin wasu filaye don su bar inda suke.

Da zarar damuna ta wuce, mutanen sai su sake dawowa wurin bolar.

Nan ne wurin da ya fi mu su kusa da birni, da samun kayan ‘Jari bola’ dan saidawa, wasu lokutan kuma sukan samu kayan abinci na gwangwani da manyan shaguna suke zubarwa dan lokacinsu ya wuce. Ko dai dan su ci, ko kuma saidawa.

Gwamnati ta sha daukar alkawarin za ta rufe wurin bolar baki daya, amma har yanzu hakan ba ta samu ba.

Rashin rufe wurin ya sanya, har yanzu mutane su na zaune a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, hukumomin sun ce a baya sun ce mazauna yankin su fice daga nan saboda gine-ginen da suka yi ba bisa ka’aida ba ne amma shiru babu alamun za su tashi.

Wani mazaunin yankin da dansa ya ji rauni sakamakon zaftarowar bolar, ya shaidawa BBC cewa ba shi da wurin da zai koma idan ya bar unguwar, idan gwamnati ta bukaci su koma wani wuri da suka tallafa musu ginanne babu abin da zai sa ya ci gaba da zama a wurin mai cike da hadari.

An sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a brnin Maputo tun daga ranar Lahadi da ta wuce, hakan ya janyo ambaliyar ruwa da lalata gidajen jama’a.

A yankunan da matalauta suka fi yawa a birnin Maputo, wasu mutane na zaune ne a filayen da ba nasu ba, da fatan za su samu aikin yi kafin su tashi.

Haka kuma gine-gine a gefen bolar na cike da hadari saboda kamuwa da cututtuka kamar amai da gudawa.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi