Labarai Najeriya

Buhari na kaunar ‘yan Igbo – Lai Mohammed

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya ya ce gwamnatin kasar na samun nasara a yakin da take yi da cin hanci da rashawa.

Alhaji Lai Muhammed ya ce gwamnatin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai akan duk wata kungiyar mai tada zaune tsaye a kasar.

Ya kuma nanata cewa shugaba Buhari na da koshin lafiyar ci gaba da mulkin kasar.

Alhaji Lai Mohammed ya yi wadannan bayanan ne a yayn wata ganawa da yayi da shugaban sashin Hausa na BBC Jimeh Saleh a birnin Landan.

A kan batun dalilin da ya sa har yanzu aka ji shiru game da bincike kan zargin cin hancin da aka yi wa sakataren gwamnatin Buhari, Babachir David Lawal, ministan ya ce: “Bai zauna a kan rahoton ba, kuma na tabbata cewa zai bayyana sakamakon binciken, da hukuncin da ya yanke a lokacin da ya shirya”.

Ya kara da cewa “Abu mafi muhimmanci shi ne bai yi wata-wata ba, ya dakatar da sakataren gwamnatin tare da shugaban hukumar bincike ta NIA”.

Akan batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari ta lashi takobin aiwatarwa, ministan ya ce “Shawarar gwamnati ta kafa kotuna na musamman da zasu rika kula da masu laifukan cin hanci da rashawa, ina ganin wannan ita ce hanyar tabbatar da ana yakin a dukkan sassa na kasar nan”.

Alhaji Lai Mohammed kuma ya kare masu cewa Buhari mutum ne mai salon mulki na kama karya, wanda ba ya mutumta ‘yancin ‘yan Adam.

Karanta cikakken labari

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi