Labarai Najeriya

Daga 2008 Zuwa 2016 An Kama Jiragen Ruwa 200 A Tekun Najeriya

VOA Hausa
Daga VOA Hausa

An gudanar da wannan taron ne a jihar Legas ta Najeriya wacce na daya daga cikin membobin kungiyar. Mahalarta taron sun yanke shawarar daidaita dokokin kasashen da ke cikin hadakar da nufin gaggauta hukunci da kuma kawo karshen auyukan fasa kwauri da fashin cikin teku a yankin ruwan na Guinea, kamar yadda Mista Alan Charles na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Ya kuma bayyana cewa akwai ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniyan da suka kai akalla guda hamsin da ke wannan yankin tekun. Wata ma’aikaciyar shari’a ta Najeriya Hajiya Hajara Yusuf na cikin masu jawabi a wajen taron, don bayyana matsayin da kasarta ke ciki na daukar matakan shari’a akan wadanda ake damkewa da laifi.

Shima wani jami’in sijan ruwa Adimiral Ferguson, kwamandar horarwa a rundunar sojan ruwan ta Najeriya, ya bayyana cewa sun zage damtse don magance mfashin teku.

Inda ya bayyana cewa a daga shekarar 2008 zuwa ta 2016 an kama jiragen da ke da laifi akalla guda dari biyu, amma wadanda aka hukunta bas u wuce guda goma sha biyar ba.

Game da mai rubutu

VOA Hausa

VOA Hausa

Aiko da Ra'ayi