Duniya Labarai

Donald Trump ya amince da birnin Kudus

DW Hausa
Daga DW Hausa

Shugaban Amirka Donald Trump ya amince a hukumance da birinin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, wanda ya ce za a mayar da ofishin jakadancin Amirka daga Tel Aviv zuwa birini na Kudus.

Gabannin sanarwar da ya bayyana shugaban na Amirka ya bayyana cewar an dade ma ba amince ba da bayyana birnin na Kudus ba a matsayin babban birnin Isra’ila. Tuni dai da wannan sanarwa ta shugaban ta fara janyon ka ce na ce a duniya. MDD da China da Birtaniya sun bayyana fargabansu a game da matakin.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi