Duniya Labarai

Donald Trump ya shiga halin tsaka mai wuya

DW Hausa
Daga DW Hausa

Sakamakon yadda Roy Moore dan jam’iyyar Republican ya fadi a zaben kujerar majalisar dattawa a jhar Albama a gaban dan jam’iyyar Democrat Doug Jones.

Nasarar ta Doug Jones wacce ta zo bazata, ita ce nasara ta farko da jam’iyyar Dmocrat ta samu a Jhar Albama a cikin kusan shekaru 25. Roy Moore wanda ke da goyon baya shugaban Amirkan Donald Trump an sha yi masa zarge-zarge na cin zarafi wasu ‘yan mata. Da wannan nasarar da jam’iyyar ta Democrat ta samu za ta iya samun rinjaye da kujeru 51 a zaben zauren majalisar dattawan a shekara ta 2018.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi