Duniya Labarai

Gobarar Daji Ta Kashe Akalla Mutane 10 a Jihar California dake Amurka

VOA Hausa
Daga VOA Hausa

A kalla mutane 10 ne suka mutu yayin da gobarar daji ke ta kone wani yanki na jihar California ta Amurka, a cewar shugaban ‘yan kwana-kwana jiha Litinin.

Ofishin ‘yan sandan garin Sonoma ya kafe a Twitter cewa an samu rahotan mutuwar mutane bakwai a dalilin gobarar.

Gobarar dai ta lakume gidaje da wuraren kasuwanci sama da 1,500 yayinda mutane da yawa suka raunata, wasu kuma ba a san inda suke ba, duk a sanadin tashin wutatai kashi-kashi har 14 a cikin wasu kananan hukumomi uku dake Arewacin jihar California.

An dai samu kwashe mutane dubu ashirin, ciki har da daruruwan marasa lafiya daga asibitocin yankin.

Ma’aikatar kare gandun daji ta California ta ce an fara binciken abin da ya haddasa tashin gobarar.

Game da mai rubutu

VOA Hausa

VOA Hausa

Aiko da Ra'ayi