Labarai Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce wasu ‘yan siyasa na da hannu a rikicin Filato

DW Hausa
Daga DW Hausa

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta ce masu takama da siyasa na da ruwa da tsaki a cikin rikicin jihar Filato da ya ta da hankali a daukacin kasar.

Ya zuwa yammacin ranar Litinin gwamnatin kasar ta tura wata babbar tawaga a karkashin mataimaki na shugaban kasar ya zuwa jihar Filato da nufin yin jaje da ma kara sanin abin da ya faru a karshen mako a wasu yankuna na jihar.

Majiyoyi daban-daban kama daga hukumomin tsaron kasar ya zuwa masu gani su fada sun tabattar da kwararar jini tudai da gangare na Filato a wani abin da ya ta da hankali ke kuma nunin jan aikin da ke gaban mahukunta na kasar a gaba.

Wata sanarwar fadar gwamnatin kasar da ranar wannan Litinin ta zargi masu ruwa da tsaki da siyasa da ta’azzarar rikicin da a fadar kakaki na gwamnatin Mallam Garba Shehu, “ya faro ne daga satar shanu sama da 100 ya kuma rikide ya zuwa zubar jinin da ba ta misaltuwa.”

Taro tsakanin Buhari da malaman Musulunci don gano mafita

Shi kansa shugaban kasar ya share kusan tsawon awoyi guda biyu yana wata ganawar sirri da manyan malaman addinin Islama da suka zo domin tattauna batun rashin tsaron da ma ba da shawara ga gwamnatin.

Kuma a fadar Yakubu Musa Hassan Katsina da ke zaman daya a cikin malaman da suka ziyarci Buharin “gazawar gwamnatin kasar na hukuncin laifi na da ruwa da tsaki da kara ta’azzarar rikicin.”

Tuni dai ta da hankalin na Filato ta fara jawo muhawara mai zafi cikin kasar, inda kungiyar Kiristoci ta kasar ta zargi gwamnatin tarrayar da kokari na kare musu dangi.

Zargin kuma da a fadar Dr Khalid Aliyu da ke zaman sakataren kungiyar Jama’atul Nasaral Islam ta kasar ke kama da kokarin ta da husuma.

An dai zura ido a ga tasirin zaman kokarin mahukunta na shawo kan tarin rigingimu a daidai lokacin da kasar ke kara kusantar zabe na 2019.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi