Labarai Najeriya

Hare-hare sun kashe rayuka a Najeriya

DW Hausa
Daga DW Hausa

Wasu jerin hare-hare da wasu suka kaddamar sun yi sanadin salwantar rayukan jama’a tare da jikkatar karin wasu a yankin arewa maso gabashin Najeriya mai fama da matsalar tsaro.

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kaddamar da hare-hare a wata kasuwa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inda kimanin mutane 20 suka salwanta wasu sama da hakan kuwa suka jikkata. Hare-haren da suka auku da almurun jiya Juma’a, sun faru ne a garin Konduga kimanin mil 20 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Rundunar ‘yan sandan Bornon, ta bakin kakakinta Joseph Kwaji, na zargin maharan mata ne. Ta’asar dai na zuwa ne makonni da shari’ar wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne da ke gwagwarmaya da makamai a Najeriyar.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi