Labarai

Hatsarin Mota Ya Hallaka dan wasan Kano Pillars Chinedu Udoji

Daga Labarai

Chinedu Udoji ya gamu da mummunan hatsarin mota inda ta yi ajalinsa a hanyarsa to komawa gida daga ziyarar da ya kaiwa abokansa na Enyimba. Hatsarin dai ya faru ne cikin daren ranar Lahadi.

Chinedu Udoji ya buga wa Kano Pillars wasa a ranar da suka kara da Enyimba a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.

Kano Pillars dai ta sanar da mutuwar tasa a shafukanta na Twitter da Facebook. Su ma mabiya shafukan sada zumunta sun aike da sakon gaisuwarsu ciki har da Tsohon mataimakin Shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar, da ofishin yada labarai na fadar shugaban kasar Nigeria, da sauransu.

Chinedu Udoji dai ya mutu ya bar ‘ya’ya biyu maza da mata daya.

Game da mai rubutu

Labarai

Aiko da Ra'ayi