Addini

Kun san alkhairan da ke cikin kwanaki 10 na watan Zul-Hajji?

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Aikin Hajji daya ne daga cikin shika-shikan musulunci guda 5, da Allah SWA ya umarci dukkan musulmai gudanar da shi akalla sau daya a rayuwarsa.

Aikin Hajji ya wajaba akan wanda ya ke da lafiyar jiki, da lafiyar yin tafiyar, da kuma abin da zai yi guzuri da shi, tun daga yin tafiya zuwa kasa mai tsarki (makka) daga duk inda ya ke a duniya.

Haka kuma da guzurin da za a barwa iyali dan su ci da shayarwa, a lokacin da mutum ya yi tafiyar dan kar ya bar su cikin halin kunci.

Allah SWA bai hallatawa wanda ba shi da ikon zuwa dan yin aikin Hajji ba, dan haka ba a cin kudin bashi a tafiya don sauke faralli.

Sai dai ya halatta ga musulmin da ya ke da wata kadara da ya ke son saidawa da nufin amfani da kudin dan biyawa kan shi zuwa birnin Makka dan gudanar da aiki.

Haka kuma ya halatta musulmi ya karbi kudi bashi da niyyar idan ya dawo daga aikin Hajji, ya karbi wasu kudi bashi idan ya dawo ya biya wannan kudi da ya ci bashi.

Sheikh Hussain Zakariya malamin addinin musulunci ne a Abuja babban birnin Najeriya, ya kuma tsakuro kadan daga cikin falalar aikin Hajji.

Aikin hajji ya kunshi abubuwa da yawa, baya ga kasancewarsa daya daga cikin shika-shikan addinin musulunci guda 5, ya kuma kasance wani lokaci na yin ibada tun daga amfani da kudin da za a yi tafiyar zuwa, ibada ce ta lokaci sannan ibada ce ta ilimi.

A ranar 8 ga watan Zul-Hajji, an so wanda ya samu damar tafiya aikin Hajji, ya tanadi abinda zai ci a ranakun da za’a yi na zaman Muna, da fita Arfa.

A ranar 9 ga watan Zul-Hajji ake fita yinin Arfa, Allah SWA ya ce tsayuwar Arfa ita ce aikin Hajjin, duk wanda bai tsaya a wannan rana ba ba shi da aikin Hajji.

Bayan saukowa daga Arfa an jifa a Jamrat, akwai dawafin da aka halattawa wanda ya yi aikin Hajji yin sa wato Da’afil Ifadha, da ake so mahajjaci ya yi shi tare da sa’ayi ko dai kashegarin Sallah, ko kuma kafin ficewa daga kasa mai tsarki zuwa komawa gida kuma ya na da kyau ka dauki niyyar aikin Hajjin da mutum zai ya.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi