Duniya Labarai

Mahawara kan makomar kasar Yemen

DW Hausa
Daga DW Hausa

Bayan kisan gillar da ‘yan Houthi suka yi wa Shugaba Ali Abdallah Saleh na kasar Yemen, masu ruwa da tsaki kan rikicin kasar da ma manazarta na mayar da martani a kai, da ma kan makomar kasar.

Kashe tsohon shugaban kasar ta Yemen, Ali Abdallah Saleh, dan shekaru saba’in da biyar, da ‘yan Houthi su kai a ranar Litinin, bayan ya mulki kasar na tsawon shekaru 33 kafin ya yi murabus a shekarar 2012 ya danka mulkinta ga mataimakinsa Abdurabbu Hadi Mansur, na ci gaba da jawo martini mabanbanta tsakanin yan kasar. A yayin da wasu ke jajantawa, wasu kuma ke nuna takaici, wasu kuwa murna suke, cikinsu hadda Dr Nadiya Sulaimi, wata mai sharhi kan lamuran kasar:

“Wannan mutumin da ya kware wajen yin badda bami, wanda ake kira dila sarkin wayo, bayan da ya tsallake yunkurin kasheshi da yi mar juyin mulki sau tari, wanda kuma ake wa kirari da mai wasan maciji, saboda iya taron aradunsa da ka, dubunsa ce ta cika, saboda kwadayin mulkinsa da cutar da al,ummar Yemen da ya yi. Don haka yanzu dara ce ta ci gida, yadda yan Houthi da ya yi kawance da su suka kasheshi, bayan da Saudiya ta yi mar shigo-shigo ba zurfi.”

Koda yake, galibin masharhanta sun fi mai da hankali ne kan makomar kasar ta Yemen, bayan kashe wannan mahalukin da ya yi shekaru yana jan zarensa a siyasar kasar. Su dai ‘yan Houthi, wadanda Ali Abdallah Saleh ya danka musu fadar mulkin kasar ta Yemen Sanaa, a farkon kawancensu da shi, a yanzu suna ganin kakarsu ta yanke saka, bayan da suka yi nasarar kashe kadangaren baki tulun da ya raba kafa tsakaninsu da makiyansu, kamar yadda suka yi nasarar samun goyan bayan kusan rabin ‘yan jami,iyar tsohon shugaban. Dama dai galibin ‘yan arewacin kasar ta Yemen, sun dawo daga rakkiyar kawancen Saudiyya, saboda ritsawa da yake ta yi da fararan hula a yankunansu, don haka ne ma shugaban kungiyar ta ‘yan Houthi, Abdul Malik Al-Huthi ya siffanta yanayin da za su tunkara a gaba da yanayin samun cikakken yanci:

“Yanzu mun ketare siradin fadawa cikin wata babbar masifa. Mun lalata makarkashiyar wargaza kasar Yemen.Yanzu lokaci ne na dawo da zaman lafiya da hadin kai tsakanin yan kasa.”

A daura da haka, bangaren kawancen Saudiyya, wacca ta sha alwashin ci gaba da yakar ‘yan Houthin har sai ta ga bayansu, na fuskantar mummunan rudani, sakamakon wani shiri da Daular Larabawa ke yi na maye gurbin shugaban kasar na jeka na yika, Abdurrabbul Hadi Mansur, wanda ake zargin Saudiyyar na yi mar abun da ya yi kama da daurin talala a kasarta, za ta maye gurbinsa da dan marigayin, Ahmad Abdullah Saleh.

A yanzu haka dai, duk da rashin sanin tabbatacciyar makoma ga kasar ta Yemen, yaki ya sake dawo ruwa a kasar, yadda kawancen Saudiyya ke ci gaba da yin lugudan wuta kan birnin na Sanaa, ba kakkautawa, a yayin da kasar Iran da ke goyan bayan ‘yan Houthi ta ce a shirye take ta taimaka wa al,ummar Yemen yakar sojojin mamayar da ke neman danka ragamarsu ga Amirka. lamarin da ke kara jefa al,ummar kasar ta Yemen da ba ta san hawa ba ta san sauka ba cikin muwuyacin hali.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi