Labarai Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Gano Kurakurai A Kasafin 2018

VOA Hausa
Daga VOA Hausa

Mafiya yawan lokuta hasashen kasafin kudin Najeriya yana yawan dogara da kudaden shige da ficen kudin danyen man fetur din kasar wanda shine babban arzikinta.

Amma ita gwamnatin Shugaba Buhari mai ci a yanzu, ta lashi takobin rage dogaron kasafin kudin Najeriya akan danyen man fetur tunda kasar na da albarkatun dogara akai da yawa, sannan kuma ga kalubalen da ke fuskantar harkar ta man fetur a duniya na fadi tashin farashin mai, da kuma tashin tashinar da ake samu tsakanin ‘yan tada kayar bayan da ke gadara da man na fitowa ne daga bangarensu.

Baya ga zargin aringizo ko cushe a kasafin kudin Najeriya a wasu lokutan da suka gabata, in ba’a manta ba an yi ta cece-kucen da wasu suka kalla a matsayin abinda ya haifar da jan kafar a tattalin arzikin kasa da kuma walwalar al’umma.

Kasafin kudin na badi shine mafi yawa da zai lashe makudan kudade don ganin cewa kasar ta yiwa matsalar tattalin arziki kwaf daya don amfanin al’ummar kasar tare da magance bakin talaucin da yake addabar ‘yan kasa game da rayuwar yau da kullum.

A zaman da Majalisar tayi ya nuna cewa, sun gano wasu kurakurai da ke bukatar a waiwayesu da gyarawa don kar ayi kitso da kwarkwata a kasafin na shekarar da ke tafe.

Wasu daga masu ruwa da tsaki game da kasafin kudin sun tofa albarkacin bakinsu game da yadda suke kallon lamarin kasafin kudin na badi, a cikin rahoton da Wakiliyarmu Medina Dauda ta aiko mana daga zauren na Majalisa da ke Abuja.

Game da mai rubutu

VOA Hausa

VOA Hausa

Aiko da Ra'ayi