Wasanni

Man City ta bayar da tazarar maki biyar

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Kungiyar Manchester City ta bai wa Manchester United tazarar maki biyar, ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier, bayan da ta ci Burnley 3-0 a ranar Asabar.

City ta fara cin kwallo ta hannun Sergio Aguero a bugun fenariti, kuma na 177 da ya ci wa City tun komawarsa can da taka-leda.

Hakan ne ya sa ya yi kan-kan-kan da Erik Brook wanda tun farko ya ci 177 tsakanin 1928 zuwa 1939 a kungiyar ta Etihad.

Daga baya ne Nicolas Otamendi da kuma Leroy Sane suka ci wa City sauran kwallayen da suka bai wa kungiyar damar hada maki uku rigis a fafatawar.

City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier da maki 25, yayin da Manchester United wacce Huddesfield ta doke ta 2-1 ke ta biyu da maki 20.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi