Wasanni

Man City ta yi nasara a gidan Man Utd

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Manchester City ta yi nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United a wasan da suka yi gumurzu ranar Lahadi inda suka tashi wasan 2-1.

David Silva ne ya fara zura kwallo a ragar Manchester United a minti na 43 da fara fafatawar, yayin da Marcus Rashford ya farke wa kungiyarsa a minta na 45.

Bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ne Nicolas Otamendi ya kara zabga kwallo ta biyu a ragar Manchester United a minta na 54.

City ta ci gaba da zama ta daya a teburin firimiya da tazarar maki 11 tsakaninta da mai bi mata baya Machester United.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a gasar a ranar Lahadi su ne:

  • Southamton 1-1 Arsenal
  • Liverpool 1-1 Everton

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi