Wasanni

Manchester City ta doke Arsenal 3-0 ta ci kofin Carabao

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Manchester City ta ci kofinta na farko kakashin jagorancin Pep Guardiola, inda suka caskara Arsenal 3-0 a wasan karshe na kofin Carabao (EFL), wanda karo na uku ke nan da ya gagari Arsene Wenger, a filin wasa na Wembley.

Sergio Aguero ne ya fara daga ragar Arsenal minti 18 da fara wasa haka aka ci gaba da taka leda hai sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci kyaftin din City Vincent Kompany ya kara ta biyu a minti na 58.

Haka kuma bayan minti bakwai sai David Silva ya biyo baya da ci na uku da bal din da Danilo ya ba shi.

‘Yan Arsenal dai ba su taka wata rawar a-zo-a-gani ba a wasan in ban da wani hari da Pierre-Emerick Aubameyang ya kai tun ana farko-farkon wasan kafin a fara cinsu.

Wannan kofin na League shi ne har yanzu kofin Ingila wanda Arsene Wenger bai dauka ba a Arsenal, wanda wannan shi ne karo na uku da yake kuskurewa a wasan karshe a shekara 21 da yake jagorantar kungiyar.

Guardiola, wanda kungiyarsa Manchester City take jagorantar gasar Premier da tazarar maki 13, ya sake makala alamar nan ta dan zirin kyalle mai ruwan dorawa ta nuna goyon bayan ‘yan awaren yankin Kataloniya na kasarsa Spaniya wadanda aka daure, abin da a baya ya jawo masa fushin hukumar kwallon kafa ta Ingila.

A kaka ta biyu da ya yi yanzu a City, ya ci kofin na League (EFL), wanda zai zama kari a kan kofuna 21 da ya ci a matsayin kociya a Barcelona da Bayern Munich.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi