Wasanni

Manchester City ta kara zama daram bayan doke Swansea 4-0

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Jagorar Premier Manchester City ta ci gaba da bajintarta ta cin manyan wasanninta a jere zuwa 15, inda ta caskara ta karshe a tebur Swansea da ci 4-0.

David Silva ne ya fara daga ragar masu masaukin a minti na 27 da shiga fili kafin kuma Kevin de Bruyne ya ci ta biyu a minti na 34.

Daga nan kuma sai bayan hutun rabin lokaci aka ci gaba da daga ragar ta Swansea inda Silvan ya jefa ta uku, wadda ita ce ta biyunsa a minti na 52, sai kuma Aguero ya kammala da ta hudu a minti na 85.

Da wannan nasara Manchester City ta kara tabbatar da ratar maki goma sha daya da ke tsakaninta da abokiyar hammaya Manchester United ta biyu a tebur.

Ita kuwa Swansea rashin nasara na shida a gida a wasa tara na gasar ta Premier a bana ya kara tabbatar da su a kasan tebur da maki biyu tsakaninsu da tsira daga faduwa a gasar.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi