Addini

Matsalolin aikin Hajji a Najeriya da Nijar

DW Hausa
Daga DW Hausa

A shekarar bana mutane da dama ne ba za su samun yin aikin hajji ba a Najeriya da Nijar, duk da cewar sun riga sun biya kudadensu amma kuma har yanzu ba su samu tafiya ba.

Misali a Nijar mutane kamar dubu uku ne har yanzu suke jibge a filin jirgin samar birnin Yamai suna jiran gawon shannu, bayan sun riga sun biya kudadensu amma har yanzu jiragen da za su kwashe mutane sun gaggara. Yayin da a Najeriya ma a wasu Jihohin irin su Bauchi da Adamawa aka samu karancin jirangen saman domin kwashe maniyantan zuwa kasa mai tsarki. Hakan na zuwa ne daf da lokacin da ake shirin rufe karbar maniyanta a kasa mai tsarki.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi