Wasanni

Mourinho ya ce David de Gea gwani ne

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce rawar da mai tsaron ragar kungiyarsa David de Gea ya taka ya nuna cewa shi fitaccen mai tsaron raga ne a duniya, bayan da United ta lallasa Arsenal da ci 3-1.

Dan kasar Spaniyan ya ture kwallo sau 14 a wasan, wanda hukumar tattara alkaluma ba ta taba samun haka ba a tarihi.

Mourinho ya kara da cewa, “kana bukatar mai tsaron raga ya zama cikin shiri a lokacin da kungiya take bukatarsa”.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce, rawar da De Gea ya taka ya cancanji a yaba mishi.

Sau 33 Arsenal tana kai hari ragar Manchester United, amma kwallo daya ce kawai ta shiga ragar golan.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi