Addini Duniya Labarai

Mutum miliyan biyu za su yi aikin hajjin bana

DW Hausa
Daga DW Hausa

Bayan kammala sallar asubahin wannan safiya ta Laraba ce alhazan da suka isa Saudiyya suka fara kama hanyarsu ta zuwa Muna domin fara aikin hajji gadan-gadan.

Hukumomin Saudiyya dai sun ce kimanin mutum miliyan biyu ne za su sauke farali a aikin hajjin na bana ciki kuwa har da ‘yan kasar Iran wanda a bara ba su halarci aikin hajjin ba saboda rikicin diflomasiyya tsakanin Tehran da Riyadh, sai dai a wannan karon za a yi aikin ba tare da ‘yan kasar Katar ba saboda sabanin da ke akwai tsakanin kasashen biyu wanda ya sanya wasu kasashen larabawa suka maida ita saniyar ware.

Ma’aikatar da ke kula da aikin hajji a kasa mai tsarki ta ce ta dauki dukannin matakan da suka kamata na ganin ba a samu irin ibtila’in da aka gani a shekaru biyun da suka gabata ba inda dubban mutane suka rasu sakamakon turmutsutsu da aka yi. An dai girke jami’an tsaro kimanin dubu 100 da kuma motocinsu da kayan aiki domin ganin aikin hajjin ya gudana lami lafiya kamar dai yadda mai magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Janar Mansur al-Turki ya shaidawa manema labarai.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi