Labarai Najeriya

Najeriya: An kafa kwamitin gano ‘yan matan Dapchi

DW Hausa
Daga DW Hausa

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kafa kwamiti na musanman don gudanar da bincike kan sace ‘yan matan sakandaren Dapchi da ke a jahar Yobe, acewar ministan yada labaran kasar Lai Mohammed.

Ministan yada labaran kasar ya yi karin bayani kan kwamitin wanda zai kasance karkashin jagorancin wani manjo janar, zai gudanar da aikin binciken sanin yadda aka sace ‘yan matan ya zuwa samar da shawarwarin don gano inda suke. A makon da ya gabata ne aka sace ‘yan matan dari da goma, masu shekaru tsakanin goma sha daya zuwa sha tara, an kuma zargi mayakan kungiyar Boko Haram da sace su daga makarantan kwanan da ke a Dapchi.

Batun sace ‘yan matan ya ja hankalin duniya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bakin kakakinta Stephane Dujarric, ya nemi mahukuntan Najeriya da su gaggauta ‘yanto daliban da kuma hukunta wadanda ke da hannun a sace su.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi