Kasuwanci Labarai Najeriya

Nigeria ta fara murmurewa – Farfesa Sheka

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Wani masanin tattalin arziki a Nijeriya, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce tattalin arzikin Nijeriya na tafiyar hawainiya bayan hukumar kididdiga ta ce kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta yi fama da shi.

Masanin ya ce idan tattalin arziki yana bunkasa da kashi daya ko biyu ko uku, to hakan na nufin yana tafiyar hawainiya kenan, “wanda shi ma matsala ce”.

Wani rahoto da Hukumar Kididdiga a Nijeriya ta fitar ne ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada.

Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekara ta 2017 idan aka kwatanta da rubu’i na biyu na 2016.

Farfesa Garba Sheka ya ce idan zai kwatanta yanayin da ake ciki, shi ne tamkar maras lafiya ne ya je asibiti aka yi masa gwaji, tare da ba shi magani.

“An karya lagon cutar, amma akan dauki lokaci kafin mutum ya murmure ya yi karfi,” in ji Farfesa Sheka.

Ya ce a halin yanzu matasa marasa aikin yi da kuma mutane da ke cikin matsin rayuwa, ba a yau ko gobe ne za a fara jin sauki ba.

“Samar da ayyukan yi, abu ne mai wahala don kuwa akwai akalla matasa miliyan ashirin da biyar da ba su da aikin yi (a kasar),” in ji Sheka.

Masanin ya ce jazaman ne gwamnati ta tallafa wa matasa ta hanyar koya musu sana’o’in dogaro da kai da kuma ba su jari.

A cewarsa hakan ita ce hanya mafi dorewa don kuwa gwamnati ba za ta iya samar musu aiki ba, kuma dogaro da daukar aiki daga kamfani ba ko da yaushe ne ake samun nasara ba.

“Amma mutum ya dogara da kansa, wannan ita ce hanya mafi dacewa.”

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi