Labarai Nijar

Nijar: Muhawara kan tasirin ziyarar Macron

DW Hausa
Daga DW Hausa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya soma wata ziyarar yini biyu a Nijar inda batun tsaro da na ‘yan gudun hijira za su kasance a sahun na batutuwan da shugabannin kasashen biyu za su tattauna.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da Shugaba Macron ya kai kasar ta Nijar tun bayan hawansa mulki. Batun tsaro da na ‘yan gudun hijira na daga cikin muhimman batutuwan da shugaban zai tattauna da tare da takwaransa na Nijar Mahamadou Issoufou a lokacin wannan ziyara. Kazalika Shugaba Macron zai gabatar da wani bangare na bukukuwan Kirsmetinsa tare da sojan rundunar sojin Faransa da ke Nijar.

Sai dai ga manazarta al’amurran yau da kullum musamman ma sha’anin tsaro a kasar ta Nijar kamar su Alkassoum Abdourahmane na ganin wannan ziyara ta Shugaba Macron na da nasaba da kokorin da ya ke na maido da martaba da kuma kimarsa a idanun sojojin kasar ta Faransa tun bayan da babban hafsan sojan kasar ta Faransa ya yi murabus a bisa zargin Shugaba Macron da kin sakin kudade a fannin aikin soja da na tsaro a kasar.

Kazalika ziyarar ta Shugaba Macron a Nijar na a matsayin wani goyon baya ga gwagwarmayar da kasar ta ke yi wajen tunkarar matsalolin tsaro da farmakin ‘yan ta’adda baya ga kokowar bukasa tattalin arzikinta da inganta rayuwar jama’a. Ko a baya bayan nan dai kasar ta Franasa ta bayyana gudumawar kudade euro miliyan 400 don dafa wa tsarin cigaban kasar na ”PDES” da Nijar din ta gabatar a babban taron koli na birnin Paris.

Akalla sojan Faransa dubu hudu ne ke girke a kasashen yankin Sahel karkashin rundunar Barkhane tare da jiragen yaki takwas da wasu shida na dakon kaya baya ga wasu marasa matuka akalla 5 na leken asiri da nadar bayanai da motocin yaki masu sulke da marasa sulke kimanin 600. A gobe Asabar ne shuwagabannin biyu za su jagoranci wani taron manema labarai a fadar shugaban kasar ta Nijar.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi