Labarai Nijar

Nijar: Zanga-zangar kasafin kudi ta yi muni

DW Hausa
Daga DW Hausa

Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar ke fitowa da yin kakkausar suka ga wata zanga-zangar da kungiyoyin farar hula suka shirya duba da yadda zanga-zangar ta kazanta da rikidewa ta koma dauki ba dadi tsakanin jami’an tsaro da taron darurwan jama’a da suka fito don nuna bacin ransu inda kuma suka bukaci zanga-zangar ta wuce har zuwa harabar majalisar dokoki.

Malam Bazoum Mohamed shi ne ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar a wata hira da tashar DW ya ce tafiyar demukradiyya ce ta baiwa ‘yan farar hular yin zanga-zanga sai dai yadda wasu ‘yan siyasa suka so amfani da ‘yan kungiyar farar hula sun kona majalisa ba za a lamunta ba.

Zanga-zangar dai duk da yake ta munana wasu cikakkun rahotanni daga gwamnatin kasar sun ce ba ta kai ga hasarar rayuka ba to amma anyi asarar dimbin dukiyoyin jama’a da raunata mutane galibi jami’an tsaro inji ministan cikin gida Bazoum Mohamed.

Duba da duk wadannan matsalolin da suka kawo cikas ga harkokin rayuwar jama’a ta yau da kullum sakamakon zanga zangar gwamnatin kasar ta Nijar ta ce za ta dauki wasu kwararan matakai a cikin dan takaitaccen lokaci da suka hadar da rushe kungiyar, sannan a kama wadanda suka jawo asara ta hanyar kona bangaren majalisa da jaza wa al’umma asara don su gurfana a gaban shari’a.

Tuni hukumomin suka ce sun fara tattaunawa da kungiyoyin malaman addinin Muslunci dangane da matsalar haraji kan gado da ita ma ke neman ta dauki wani sabon salo duba da rashin fahimtar da ke neman ta samu gindin zama tsakanin gwamnati da malaman, lamarin da ya kai ga kame wani malami da ke wa’azi kuma a ke cigaba da rike shi a hannun hukuma.

Daruruwan jama’a ne dai suka yi cincirindo a ranar Lahadi don nuna takaicinsu da rashin jin dadi ga sabon kasafin kudin da gwamnatin ta gabatarwa ‘yan majalisa sakamakon wasu kare karen haraji da sabon kasafin ya kumsa. Zanga-zangar da tuni wadanda suka shiryata suka kirata da ta shiga tarihi sai dai sun koka da irin yadda ta rikide ta koma irin ta ba ta kashi tsakanin jama’a da jami’an tsaro.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi