Duniya Labarai

Saudi Arabiya za ta bari a bude gidan kallo a karon farko cikin shekaru 35

Avatar
Daga Labarai

Saudi Arabiya ta cire haramcin bude gidan kallo na tsawon shekaru 35 ranar Litinin, hakan ya jawo murna daga masoya kallon fina-finai da kuma masu kamfanonin gidan kallo da suke shirin shiga domin a dama da su.

Gidajen kallon za su fara nuna fina-finai daga watan Maris na shekarar 2018, matakin yana cikin canje-canje da gwamnatin Saudiya take yi domin zamanantar da kasar. Hakan ya sa an fara gudanar da tarukan kade-kade da wake-wake, sannan kuma mata sun fara karbar lasisin tuka mota wanda a baya ya haramta.

Gwamnatin Saudiyar dai ta haramta gidajen kallo ne a shekarar 1980, saboda bukatar da masu tsaurin addinin musulunci suke nunawa a wancan lokacin, wanda ya sa suka haramta shakatawa a bayyane da kuma haduwar maza da mata a waje daya.

Canje-canjen da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ke yi ya saukaka abubuwa da dama a kasar, saboda suna kokarin fadada tattalin arzikin kasar da kuma rage dogaro da arzikin man fetur.

Dubban ‘yan kasar ta Saudiya dai suna tafiya kasashen makota irinsu Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain domin samun damar kallo da kuma shakatawa.

Tuni dai kamfanin haska fina-finai na gabas ta tsakiya wato ‘VOX Cinemas’ ya fara shirin bude gidan kallo a babban birnin Saudiya wato Riyadh a karon farko. Ana sa rai de wannan canjin zai sa kasar ta samu kudin shiga kimanin dalar amurka biliyan 24 zuwa shekara ta 2030.

Game da mai rubutu

Avatar

Labarai

Aiko da Ra'ayi