Labarai Najeriya

Shugaba Buhari Ba Zai Yi Murabus Ba – Yarima

VOA Hausa
Daga VOA Hausa

Duk da fatattakarsu da jami’an tsaro suka yi, yau masu fafutikar ganin shugaba Buhari ya yi murabus, sun ci gaba da zaman dirshan inda suke cewa ba gudu ba ja da baya suna nan akan bakarsu.

To saidai Majalisar Dattawan Najeriya ta mayar da martani akan wannan matsayin na mutanen dake cewa shugaban kasa ya wuce kwanaki 90 da kasancewa kasar waje saboda haka yayi murabus. A cewarsu bayan kwana 90 karya dokar kasa ce idan shugaban bai yi murabus ba.

Majalisar Dattawan Najeriya ta bakin tsohon gwamnan Zamfara Ahmed Yarima ta karyata dokar da masu fafutikar suka dogara a kai.

Sanata Ahmed Yarima yace mutanen basu san tsarin mulkin Najeriya ba. Inji Yarima tsarin mulkin kasar yace idan shugaban kasa zashi hutu ko zuwa yin wani abu muddun ya rubutawa Majalisar Dattawa mataimakinsa ya zama mukaddashinsa har ranar da shugaban ya dawo ko kuma ya rubuta wata wasikar da ta kunshi wani abu daban.

A cewar Yarima idan shugaba bai sake rubuta wata wasika ba babu majalisa ko wata doka da zata ce wa’adinsa ya kare saboda kundun tsarin mulkin kasa bai tsayar da wani wa’adi ba.

Shi ma Farfasa Al-Mustapha Usujud kwararre akan ayyukan dokoki da na majalisa yace koda ranar da aka rantsar da shugaban ya rubuta zashi jinya babu abun da za’a yi sai ranar da ya dawo. Haka tsarin mulkin kasar ya tanada.

Game da mai rubutu

VOA Hausa

VOA Hausa

Aiko da Ra'ayi