Labarai Najeriya

Shugaba Buhari ya yi tir da kisan mutum 86 a Filato

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan mutum 86 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Filato da ke arewacin Najeriya.

A yayin da shugaban ke kwantar da hankula, ya ce dukkanin wadanda ke da hannu a harin za su fuskanci hukunci.

Sabon rikici da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a kauyukan Filato ya soma ne tun ranar Alhamis da ta gabata, lokacin da aka kai wa wasu makiyaya hari, abin da ya tunzurasu ga ramakon da ya yi sanadin gwamman rayuka a ranar Asabar.

Maharan sun kai hare-hare ne da bindigogi cikin dare a kauyuka a kalla bakwai a gundumar Gashish da ke karamar hukumar Barikin Ladi na jihar ta Filato.

Shugaban karamar hukumar Barkin Ladi Mr Dickson Yusuf Chollom, ya shaida wa BBC cewa sun gano gawawwakin mutane 34 a yayin da suke ci gaba da tattara alkaluman wadanda aka kashe a hare-haren.

Ya ce lamarin ya haifar da zaman zullumi inda mutanen yankin ke kauracewa gidajensu.

Hukumomomi sun kafa dokar hana fita daga yammaci zuwa safiya a wasu yankuna na jihar domin hana bazuwar tashin hankali.

Hukumomin jihar kuma sun ce mazauna kauyukan sun yi zargin makiyaya ne suka kai hare-haren, zargin da kungiyar fulani makiyaya ta musanta.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah, a jihar ta Filato, Malam Muhammad Nurah Abdullahi, wanda ya musanta zargin yana mai cewa an kashe Fulani makiyaya guda biyar tare da kona motar da suke ciki a yankin na Barkin Ladi a ranar Alhamis.

Tuni dai gwamnatin jihar Filato ta kafa dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a kananan hukumomin Barkin Ladi da Jos ta kudu da kuma Riyom, bayan da aka shiga zaman dar-dar a yankunan.

An kafa dokar ne sakamakon rahotannin da ke cewa wasu matasa da suka fusata da kashe-kashen da aka yi a kauyukan na Barikin Ladi sun fara tare hanya suna far wa matafiya, yayin da rundunar ‘yan sandan jihar ta ce jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.

A baya dai jihar filato ta yi fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini inda dubban mutane suka rasa rayukansu.

Amma jihar ta samu kwarya-kwaryar zaman lafiya cikin fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Jama’a da dama daga bangarori daban-daban a jihar yanzu na nuna damuwa kan sabon tashin hankalin, wanda ka iya mayar da hannun agogo baya idan har masu ruwa da tsaki ba su tashi haikan ba don dakile shi.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi