Kasuwanci

Shugaban kamfanin Samsung na fuskantar shekaru 12 a gidan yari

Avatar
Daga Labarai

Shugaban kamfanin Samsung zai iya fuskantar har shekaru 12 idan masu kara sun samu yadda suke so.

Masu gabatar da karar sun bayar da bayanin rufe karbar shaida a Koriya ta Kudu a ranar Litinin, suna nuna shugaban Samsung wato Lee Jae-yong a matsayin wanda ya san abin da ya ke yi a lokacin da kamfanin ya biya miliyoyin daloli zuwa wasu kamfanonin dake da alaka da tsohon shugaban kasar.

“Ko da yake ya amince cewa yayi wasu tarurruka da shugaban kasar, ya yi ikirarin bashi da wani laifi,” mai gabatar da kara Park Young-soo ya ce, yana neman aikashi gidan yari har na tsahon shekaru 12.

Lee, dan shekaru 49, dan mai kamfanin Samsung, yace bashi da laifi a zargin cin hanci da rashawa, rantsuwar kaffara, ɓoye ribar kudin haram, almubazzaranci da kuma boye dukiya a kasashen waje.
Kuma yana da hannu a hambarar da tsohon shugaban kasar Park Geun-hye.

Mai gabatar da kara yace Lee – wanda ake kiransa da sunan Jay Y. Lee – ya bayar da cin hanci ga Park da kuma wata kawarsa, Choi Soon-sil, domin ya samu goyon bayan gwamnati akan wani yunkuri na hadewa da wani kamfani domin kara masa karfi.

A bayaninsa na karshe Lee yace wa kotun a ranar Litinin, ƙarya ake yi masa a dukkan tuhume-tuhume.

“Ban taba tambayar shugaban kasa wani abu da zai amfaneni ba, ko da a cikin sirri ne,” ya fadi hakan yana zubar da hawaye.

Kotun zata sanar da hukunci a kan lamarin ranar Agusta 25.

Hudu daga cikin manyan shugabannin Samsung su ma ana tuhumarsu da laifi, ciki har da wani shugaban Samsung Electronics, sashe mafi mahimmanci a kamfanin.

Choi, kawar tsohon shugaban kasar, an yanke mata hukumcin shekaru uku a kurkuku a watan Yuni.

An gurfanar da Park Geun-hye tun a watan Mayu. Ta musanta zargin cin hanci da rashawa, tilastawa, da kuma bayyana bayanai na sirri.

Game da mai rubutu

Avatar

Labarai

Aiko da Ra'ayi