Labarai Najeriya

Takaddamar sake komawar Atiku PDP

DW Hausa
Daga DW Hausa

Sanarwar sake komawa cikin jamiyyar PDP da Atiku Abubakar ya fitar ya haifar da takaddama musamman daga wasu ‘ya’yan jamiyyar adawar da ke kokarin dinke baraka ta rigingimun cikin gida.

Komawar tsohon mataimakin shugaban Najeriyan jam’iyyar adawa bai zo wa mutane da dama da mamaki ba, domin kuwa ungulu ce ta koma gidanta na tsamiya ba wai wani sabon gida da wasu ke hasashe ba. Shugabannin jam’iyyar PDP sun baiyana cewa suna maraba da wannan mataki da ya dauka. Atiku a na shi bangaren, ya zayyana dalillai na rashin bin doka da kai’da da ya sanya shi ficewa daga APC mai mulki.

Sai dai kuma jam’iyyar PDP ta baiyana karara a fili cewa kada fa a yi zaton za a ba shi izinin zama dan takara ba tare da hamayya ba, inda tuni shugaban kwamitin riko na jam’iyyar ta PDP Ahmed Makarfi ya fito da kubensa na bukatar neman zama dan takara. Jam’iyyar ta ce darewarsa a taragon PDP ba zai sanya a sauya tunani ba.

Da alamun cewa Atiku na fuskantar tirjiya mai karfi a tsakanin ‘ya’yan sabuwar jamiyyarsa, domin ko da furucin da ya yi cewa ya dauki matakin don kyautata rayuwar matasa, bai sanya wasunsu daga masa kafa ba.

Abin jira a gani shi ne ko jam’iyyar ta PDP za ta ba shi damar tsayawa a matsayin dan takararta ganin bisa ka’idojinta ya kamata sai ya shekara guda kafin samun wannan damar, lokaci ne zai nuna inda aka dosa.

Game da mai rubutu

DW Hausa

DW Hausa

Aiko da Ra'ayi