Afurka Labarai

Uhuru Kenyatta ne ya lashe zaben Kenya

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ne ya samu nasara a babban zaben da aka gudanar a kasar ranar Talata, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana.

Mista Kenyatta ya samu kashi 54.3 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin mai biye masa Mista Raila Odinga, ya samu kaso 44.7 cikin 100.

Sai dai gamayyar ‘yan adawar kasar sun yi watsi da sakamakon zaben tun gabanin a sanar da shi.

Masu sanya ido na kasashen waje sun bayyana zaben a matsayin sahihi wanda aka yi cikin ‘yanci da adalci.

Mista Odinga – ya yi zargin cewa masu kutse sun kutsa ciki na’urar da ke tattara sakamakon zaben inda suka sauya alkalumma.

Sai dai hukumar zaben kasar ta musanta zargin.

‘Yan takara guda takwas ne suka tsaya takara a zaben, sai dai Mista Kenyatta da Odinga ne a gaba-gaba.

Yawancin al’ummar Kenya na fargbar barkewar rikici bayan zaben, makamancin wanda aka samu a zaben shekarar 2007, inda sama da mutane 1200 suka rasa rayukansu, yayin da mutane dubu dari shida suka rasa muhallansu.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi