Labarai

‘Yan Liberia na zaben shugaban kasa

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

A ranar Talata ne ‘yan Liberia zasu fita rumfunan zabe domin su zabi sabon shugaban kasa bayan da shugaba Ellen Johnson-Sirleaf ta shafe fiye da shekara goma tana mulkin kasar.

Nan da dan karfe 7 agogon Liberiya ne za a bude rumfunan zabe a fadin kasar Liberiya domin zabukan shugaban kasar da ‘yan majalisa.

‘Yan takara 20 ne za su fafata a wannan zabe don mayen gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf wadda ita ce mace ta farko da aka zaba shugaba a Afrika.

Tuni dai shugabar mai barin gado ta yi wa al’ummar kasar jawabi inda ta nemi a yi zabuka cikin kwanciyar hankali da lumana.

Midok Sakhan, wani mazauni Monrovia babban birnin kasar ya fadawa BBC cewa zaben tsakanin manyan ‘yan takara uku ne:

“Na farko shi ne Joseph Boakai wanda shi ne mataimakin shugabar kasar mai ci a yanzu, kuma tun watan Janairun 2006 yake rike da wannan mukamin”.

Mista Sakhan ya ce mataimakin shugaban kasar na da farin jini sosai a kasar, amma matasa na ganin ya tsufa.

Na biyu shi ne George Weah, tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa, wanda ya buga wa kungiyar AC milan ta Italiya har ya samu lambar yabo ta zakaran kwallon kafa na duniya.

“George Weah na da farin jini wajen matasa, kuma ya taba tsayawa takarar mukamin shugaban kasa tare da wannan shugabar mai barin gado. Yana da babbar damar lashe wannan zaben”, inji Mista Sakhan.

Dan takara na uku shi ne Alexander B. Cummings, wanda shi ne shugaban kamfanin Coca-Cola a nahiyar Afirka.

Akwai kuma MacDella Cooper, wacce sananniya ce domin ayyukan jin kai da taimako da take yi a kasar. Tana neman ta gaji Ellen Johnson-Sirleaf.

Idan haka ya kasance, a karon farko a nahiyar Afirka mace ta gaji mace a shugabancin wata kasa kenan.

Mista Sakhan ya ce yana da yakinin cewa ba za a sami wata matsala a lkacin wannan zaben ba, “Abin lura a nan shi ne dukkan alamu na nuna cewa za a gudanar da wannan zaben cikin lumana”.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi