Wasanni

Zakarun Turai: Liverpool ta yi kaca-kaca da Spartak Moscow 7-0

BBC Hausa
Daga BBC Hausa

Philippe Coutinho ya zura kwallo uku rigis a wasan da Liverpool ta zama kungiya ta biyar ta Ingila da ta tsallake zuwa mataki na gaba na kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai inda ta yi kaca-kaca da Spartak Moscow a Anfield da ci 7-0.

Kungiyar ta Jurgen Klopp wadda ta zama jagora ta rukuni na biyar (Group E), ta shiga wasan ne da sanin cewa tana bukatar ta jajurce kada a doke ta, domin ta tabbatar da zuwanta matakin na gaba, a karon farko tun kakar 2008-09, kuma Coutinho ya sanya su gaba da fanaretin da ya ci a minti hudu da fara wasa, bayan da Georgi Dzhikiya ya yi wa Mohamed Salah keta.

Bayan minti 11 kuma sai Coutinho din ya sake cin ta biyu, bayan da Firmino ya zura masa kwallon, kafin shi ma kuma Firminon ya ci tasa a minti na 18.

Minti biyu kacal da dawowa daga hutun rabin lokaci ne sai Mané ya ci ta hudu, sannan kuma Coutinho ya cike tasa ta uku wadda ita ce ta biyar ga kungiyar.

Can kuma a minti na 76 sai Mané ya zura tasa ta biyu amma ta shida a kungiyar kafin kuma Mohamed Salah ya ci cikammakin ta bakwai a minti na 86.

Nasarar ta Liverpool ta sa wannan shi ne karon farko da kungiyoyin Ingila biyar suka tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar ta cin kofin zakarun Turai a kaka daya.

Hakan na nufin Chelsea da Manchester City da Manchester United da Tottenham za su kasance tare da Liverpool din a jadawalin gasar na zagaye na biyu da za a fitar a ranar Litinin a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, a birnin Nyon, na Switzerland, da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya.

Daga cikin kungiyoyin da za a iya hada Liverpool din da su a wasan na gaba, akwai mai rike da kofi Real Madrid ko zakarun gasar sau biyar Bayern Munich da zakarun Italiya Juventus.

Ko kuma kungiyar Basel ta Switzerland da Shakhtar Donetsk ta Ukraine da kuma Porto ta Portugal.

Game da mai rubutu

BBC Hausa

BBC Hausa

Aiko da Ra'ayi